Labarai
NAFDAC ta kama kayayyaki marasa inganci na fiye da miliyan 500 a Kano

Hukumar Kula da ingancin abinci da magani ta kasa NAFDAC ta ce ta kama wasu kayayyaki marasa Inganci a wasu kasuwanni da manyan kantinan sayar da kayayyaki a nan Kano da kudinsu ya Kai fiye da Naira Miliyan Dari Biyar.
Shugaban hukumar Mai Lura da jihar Kano,Kasim Idris Ibrahim,ne ya bayana hakan a zantawarsa da manema labarai a yau Jumma’a a shelkwatar hukumar dake sakatariyar Gwamnatin tarayya dake Kan titin zuwa Katsina a nan Kano.
Idris Ibrahim,ya Kuma ce yanzu Haka sun fara bincike Kan mutanen da suka kama da kayayyakin dan daukar mataki na gaba.
Kasim Idris Ibrahim,ya Kuma ce akwai bukatar masu siyan kayayyaki su tabbatar sun duba lambar hukumar a jikin kayan da zasu siya dama lokacin karewar amfaninsa dan kaucewar ci ko amfani da kayan da zai cutar da su.
You must be logged in to post a comment Login