Labarai
Najeriya ƙasa ce mai mutunta bambancin addinai- Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai mutunta bambancin addinai, tare da kare ‘yan ƙasar ba tare da nuna wariya ba.
Shugaba Tinubu, ya bayyana hakan ne ta cikin martaninsa bisa kalaman Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya zargi Najeriya da rashin kare addinai. Tinubu ya ce gwamnatin sa na ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmai da kiristoci a faɗin ƙasar.
Haka kuma, Tinubu, ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofi na haɗin kai, adalci da kariya ga kowa da kowa bisa tsarin doka domin tabbatar da cewa Najeriya ta zauna cikin zaman lafiya da ɗorewar cigaba.
You must be logged in to post a comment Login