Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za su dawo da zirga-zirgar jiragen sama

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bayyana yiwuwar dawo da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da hadaddiyar daular Larabawa.

Wani jami’i a kwamitin yaki da cutar corona na shugaban ƙasa Mukhtar Muhammad ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai.

Ya ce ƙasashen biyu sun amince da ƙa’idojin yin tafiye-tafiye da kuma sharuɗɗan da gwamnatin haɗaɗɗiyar daular larabawa ta sanya.

Jaridar the Cable ta rawaito cewa Mukhtar Muhammad ya kuma ce, gwamnatin tarayya ta amince ga buƙatar gwajin COVID-19 da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanya a baya a cikin Maris 2021 don kiyaye yaɗuwar ta.

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin kasashen biyu a watan Maris saboda batutuwan da suka shafi yarjejeniyar COVID-19.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!