Labarai
Nasiru Yusuf Gawuna ya yi murabus daga mukaminsa na Shugaban Hukumar FMBN

Tsohon ɗan takarar gwamna a Kano a Jam’iyyar APC na shekarar 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwa Bankin bada lamunin Gidaje na Tarayya FMBN.
A cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan watan 27 ga Maris, 2026, Gawuna ya ce matakin nasa ya fara aiki nan take, yana mai cewa ya yi hakan ne domin bin umarnin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na bukatar masu rike da mukaman siyasa su sauka bisa tanade-tanaden dokar zabe.
Gawuna ya kuma gode wa Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima, yana mai cewa mukamin ya ba shi damar bayar da gudunmawa ga ci gaban bankin da kuma kasa baki daya.
Ya kara da cewa zai tabbatar da mika ragamar aiki cikin tsari, bisa ka’idoji da dokokin da suka dace.
Saukar ta sa na zuwa ne da wasu rahotanni ke nuni da cewa Gawuna na shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ADC, bayan tattaunawa da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da babu sanarwa a hukumance kan hakan zuwa yanzu.
You must be logged in to post a comment Login