Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Nazari kan halin da yaran da aka haifa bata hanyar aure ba

Published

on

An lura cewa da yawan yaran da ake haifa bata hanyar aure ba na fuskanta kalubale na rayuwa da suka hada da tsangwama da rashin kulawa daga al’umma da kuma dangi inda wasu yaran ma ake jefar da su tun suna kanana.

Haka zalika iyayen irin wadannan yara kan fada cikin mawuya cin hali a duk lokacin da hakan ta faru.

Wannan lamarin dai yafi Kamari a yankunan arewacin kasar nan ta inda a kowane lokaci idan aka tsinci yaro ba’a bashi kulawar data kamata duk da cewa ba’asan irin baiwar da take tare da shiba.

Malaman addinai da dama na yin kira da a daina tsangwamar yaran da aka tsinta ko kuma macen da take dauke da juna biyu wanda ba ta hanyar aure aka sameshi ba.

Haka zalika yaran da aka Haifa bata hanyar aure ba na cintar kansu cikin mawuyacin hali inda suke rasa duk wata kulawa da yakamata a ce yaro ya samu daga gurin iyayen sa wanda hakan ke jawowa wasu su fada cikin wasu dabi’un da ake guda a cikin al’umma dukkuwa da ba laifin su bane.

Ta wata fuskar kuma wasu daga cikin iyaye kan taka muhimmiyar rawa wajan sanya wadannan yaran cikin matsala ta inda idan suka ga yaran su dauke da juna biyu saisu fara tsangwamarsu sannan kuma abin ya kai ga barin gidan gaba daya.

Wakiliyar mu Maryam Adam Ibrahim ta jiyo ra’ayoyin wasu mutane a nan Kano kan kalubalen da irin wadannan yara ke fuskanta, yayin da wasu ke cewa suna cikin halin ni ‘ya su.

Yadda mahaifi ya daure ‘yarsa tsawon wata guda a Kano

An cafke matar aure na yunkurin shiga da waya gidan gyaran hali

Rashin miji ne ya hanani yin aure –Maryam Yahaya

Kazalika wasu na cewa ba kasafai suke shiga jama’a ba don gudun kada a tsangwame su.

A nata bangaren Darakta a mai’aikatar dake lura da kananan yara da cigaban Mata Hajiya Binta Nuraini,  ta ce gwamnati tana baiwa irin wadannan yara kulawa da kuma basu ilimi daidai da sauran yara dake cikin al’umma.

Ita ma shugabar sashen dake lura da walwalar mata da kananan yara ta jihar Kano Hajiya Hajara Shehu Minjibir, tace bai kamata iyaye su runka korar ‘yayan su mata da suka gamu da irin wannan iftila iba kasancewar hakan na ta azzara matsalar ce kawai a cikin al’umma.

Tsohon shugaban hukumar Hisba ta karamar hukumar Gwale Malam Yahya Bala sabon Sara, cewa yayi haramun ne a musulunci al’umma wasu mutane su runka aibata irin wadan nan yara kasancewar su yaran basu da laifi a gurin A…L kasancewar an haife su ba ta hanyar aure ba.

Malam Yahya Bala Sabon Sara ya kuma ce ya zama wajibi al’umma su maida hankali wajen neman ilimin addinin musulunci don sanin hukunce hukuncen Ubangiji tare da jan hankalin maza da mata da su kasance masu jin tsoron a koda yaushe.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!