Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

NDLEA: Mun kama dillalan miyagun ƙwayoyi 89 a jihar Kaduna

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce tsakanin watan Janairu zuwa Mayu ta samu nasarar kama wasu mutane 89 wadanda ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi a jihar Kaduna.

 

Kwamandan hukumar a jihar ta Kaduna Iyke-Uche Samuel shine ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya a Kaduna.

 

Ya ce, jami’an hukumar cikin wannan wa’adi ta samu nasarar kwace miyagun kwayoyi mai nauyin kilo sama da dubu daya da dari bakwai da ashirin da daya.

 

A cewar sa, cikin miyagun kwayoyin da hukumar ta kwace sun hada da: Tabar wiwi, Tramadol, Tabar iblis, da sauran wasu miyagun kwayoyi daban-daban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!