Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NDLEA: ta cafke mutane 198 a Kano

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano na ci gaba da gudanar da ayyukanta na “Operation Hana Maye” wanda kwamanda Abubakar Idris Ahmad, CN ya ƙaddamar da nufin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

Wannan na ƙunshe ne ta a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar.

Wannan ta sa rundunar ta kama mutane da dama, da suka hada da guraren da ake sayar da miyagun kwayoyin

A yayin gudanar da aikin “Operation Hana Maye” wanda aka kaddamar a ranar 17 ga watan Junairu 2024, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta Kano ta yi nasarar cafke mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Musamman daga cikin wadanda aka kama akwai mutum 61 da ake zargi, ciki har da mata 15 da aka kama a wani gurin shaƙatawa da ake sayar da haramtattun ƙwayoyi.

Haka zalika, hukumar NDLEA ta Kano ta kama wasu mutane 42 da ake zargi da hannu a makabartar Ɗan Agundi, wanda aka bayyana a matsayin wani wurin da ake amfani da shi wajen hada magunguna, Haka kuma, hukumar ta tarwatsa guraren da ake sayar da kayan maye a makabartar Sheka da kuma sheka Obajana.

Wannan kamun ya nuna kwazon rundunar na tarwatsa hanyoyin sayar da miyagun kwayoyi da kuma kawar da wuraren safarar miyagun kwayoyi a jihar.

Haka kuma rundunar ta yi nasarar kwato wasu haramtattun abubuwa masu yawa. Waɗannan abubuwan sun haɗa da Exol 5, Sholiso, madarar sukudayin, da sauran biyagun kwayoyi daban-daban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!