Labarai
NDLEA ta yi babban kamu a Kano da wasu jihohi

Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kama hodar Iblis mai tarin yawa da aka boye cikin wasu Littattafan Addini, ta kuma Cafke wani matashi da zargin kai wa yan ‘Yan Bindiga miyagyun kwayoyi a jihar Kano tare da Kwato Fiye da Tan 2 da digo uku na Kwayoyi.
Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sahannun daraktan yada labarai da wayar da kan jumma’a na hukumar na ƙasa Femi Baba Femi, ya fitar ta kara da cewa sun samu nasarar kama wata jaka dauke da hodar iblis da aka boye a cikin littattafan addini guda 20 da ake son tura wa Saudiya daga Lagos.
Wannan kame na gram 500 ya faru ne ranar Talata, 15 ga watan nan da muke ciki na Afrilu.
Haka kuma hukumar ta kuma gano kilo 2 da digo 8 na tabar wiwi iri mai ƙarfi da ake Kira da loud da aka fi samun ta a kasaar Amurka, wadda aka gano a wani kamfanin jigila.
Sanarwar ta kuma ce, a jihar Kano ma wani matashi dan shekara 22, Muhammad Mohammed, ya shiga hanu dauke da alluran pentazocine guda 277 da ya daure a cinyarsa da gabansa, yana kan hanyarsa ta zuwa Katsina.
Haka kuma, wani mutum ya fada hannu dauke da kilo 30 na tabar wiwi.
” A Bayelsa, an kwato fiye da kilo 563 na kwayoyi iri daban-daban tare da kama mutane hudu yayin sumame a Opolo da ke birnin Yenagoa, inda a Lagos, ma aka kama mota dauke da kilo 1,100 na wiwi a yankin Surulere, a cewar sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa hukumar ta kwato kwayoyi sama da guda 31,000 a Zaria da ke jihar Kaduna, ta kuma kama kilo 97 na wiwi a Kebbi da aka boye cikin jakunkunan gawayi. A Anambra da Osun, an kama wasu da kwayoyi iri-iri, ciki har da skushi mai lita 43.
A jihar Edo, NDLEA ta lalata gonakin tabar wiwi guda biyu, inda aka hallaka fiye da kilo 3,700 na shuka.
A tashar jirgin ruwa ta Tincan, an kama Basorun Usman Kayode wanda aka dade ana nema tun bayan kama kilo 107 na kwayar Loud daga Kanada a 2023.
An kuma kama wani dillali, Dauda Yakubu a yankin tashar.
NDLEA ta cigaba da wayar da kai ta hanyar shirin yaki da miyagun kwayoyi wato WADA a makarantu, kasuwanni da wuraren sufuri.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an hukumar bisa kokarinsu wajen dakile fataucin kwayoyi da kuma wayar da kan jama’a.
You must be logged in to post a comment Login