Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NFF ta sallami Gernot Rohr ta kuma nada sabon mai horarwa

Published

on

Hukumar kwallon kafa kasa NFF ta nada Augustine Eguavoen a matsayin mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles na rikon kwarya.

Hakan ya biyo bayan sallamar Gernor Rohr a ranar Lahadi 12 ga watan Disambar 2021 da hukumar ta yi.

Rohr dai ya horar da ƴan wasan Najeriya na tsawon watanni 64.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet cewar Augustine Eguavoen zai yi aiki tare da Salisu Yusuf da Paul Aigbogun da kuma Joseph Yobo da Dakta Terry Eguaoje, yayin da Aloysius Agu zai horar da masu tsaron raga.

An kuma nada tsohon kyaftin din Super Eagles, Augustine ‘Jay Jay’ Okocha da Nwankwo Kanu da kuma Garba Lawal da za su taimaka musu.

Eguavoen tsohon kyaftin din Najeriya ya taba aikin horar da tawagar a gasar cin kofin nahiyar Afirka data gudana a kasar Masar a shekarar 2006 da Super Eagles ta yi ta uku.

Haka kuma shine kyaftin din Super Eagles da ya daga kofin nahiyar Afirka a Tunisia shekarar 1994.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!