Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nigeria: An yiwa mutum na farko riga-kafin Korona

Published

on

Wani likita mai suna Dr. Cyprian Nyong ya kafa tarihi wajen zama mutum na farko anan Nigeria da aka fara yiwa allurar rigakafin cutar Corona da jami’ar Oxford ta samar mai suna AstraZeneca.

Dr. Cyprian Nyong ya karbi allurar rigakafin ne yau a birnin tarayya Abuja.

Dr Cyprian dai ya kasance daya daga cikin likitoci da suka fara aikin yaki da cutar corona tun a shekarar da ta gabata (2020).

Yanzu dai ya kasance ma’aikacin lafiya na farko haka zalika dan Nigeria na farko da aka fara yiwa allurar rigakafin na covid-19.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko Dr. Faisal Shu’aib ne yayi masa allurar a bainar jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!