Labarai
NiMet ta fitar da sabon hasashen Yanayi

Hukumar da ke lura da hasashen yanayi ta Najeriya NiMet, ta ce akwai yuwuwar samun ruwan sama tare da tsawa na tsawon kwanaki uku a jihar Kano, inda za a fara samun yanayin daga yau Litinin.
Hukumar ta kuma ce za a samu makamancin yanayin a jihohin Adamawa, Taraba, Kebbi, Bauchi, Borno, Gombe, Katsina, Zamfara, Kaduna da kuma Yobe.
Haka kuma hukumar ta ce za a fuskanci yanayin ne da yammacin ranakun zuwa dare a kowacce rana cikin kwanaki ukun.
You must be logged in to post a comment Login