Labarai
NIPR ta yaye jami’an yada labaran Kano 71

Gwamnatin jihar Kano, ta bukaci jami’an yada labaranta na ma’aikatu da aka rantsar da su a kungiyar kwarrarrun masu hulda da jama’a ta Najeriya NIPR da su yi amfani da shaidar da suka samu wajen kara inganta aikin su da samun karin damar maki a rayuwa.
Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a lokacin da ake rantsar da Jami’an yada labaran a nan Kano.
Waiya, ya kuma godewa gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa sahalewar da ya yi na tabbatar da su a matsayin membobin kungiyar ta NIPR.
Wasu daga cikin jami’an yada labaran da aka baiwa shaidar kwarewar ta NIPR sun bayyana jin dadin su tare da godewa bisa samun wananan nasara.
Kami’an jami’an yada labarai 71 ne gwamnatin Kano ta dauki nauyin su inda kungiyar kwarrun kan yada labarai ta Najeriya NIPR, ta bai wa mutane 83 da suka yi rijistar shaidar kwarewa.
You must be logged in to post a comment Login