Labarai
NLC da TUC sun bukaci a kama kwamandan dayaci zarafin shugabanta
Ƙungiyoyin kwadago a Nijeriya NLC da TUC sun bukaci a kori kwamandan da ya jagoranci cin zarfin shugaban kungiyarsu daga aikin ɗan sanda.
Kungiyoyin sun bukaci hakan gabanin amincewa su janye yajin aiki a jiya Laraba, lokacin da suka yi wata ganawa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.
Idan za a iya tunawa a ranar 1 gawatan Nuwamba ne Ajaero tare da rakiyar wasu mambobin NLC suka shirya wata zanga-zangar a Owerri babban birnin Jihar Imo kan zargin take haƙƙin ma’aikata da gwamnatin jihar ke yi.
Gabanin zanga-zangar ta kankama ne kuma ‘yan sanda suka cafke shugaban kungiyar kwadagon kuma suka lakaɗa masa duka, abinda aka zargi gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da kitsawa.
Wannan ya ja ƙungiyoyin suka tsunduma yajin aiki domin nuna ƙin amincewa da wannan lamari.
Labaran: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login