Labarai
NLC da wasu kungiyoyi sun shawarci gwamnati kan kudaden Paris Club
Kungiyar kwadago ta kasa NLC da wasu kungiyoyin kishin al’umma sun shawarci gwamnatin tarayya da ta jinkirta batun bai wa jihohi Kason karshe na kudaden Paris Club har zuwa bayan rantsar da sabuwar gwamnati a ranar ashirin da tara ga watan da muke ciki na Mayu.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Ayuba Wabba ne yayi wannan kiran yayin zantawa da manema labarai a Abjua.
Ya ce ba daidai bane gwamnati ta bai wa jihohi makudan kudade haka a wannan lokaci da ake kokarin mika mulki wanda hakan zai sa wasa gwamnonin su yi almundahana da kudaden.
Kwamared Ayuba Wabba ya kara da cewa, a baya gwamnatin ta bai wa jihohin irin wadannan makudan kudade amma ba a sarrafa su ta hanyoyin da suka kamata ba.
Wannan shawarar yazo kwanaki kadan bayan da ministar kudi Zainab Ahmed ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba, gwamnatin tarayya za ta bai wa jihohi kason karshe na kudaden Paris Club da ya kai naira biliyan dari shida da arba’in da tara.
A nata bangaren kungiya mai rajin tabbatar da gaskiya a ayyukan gwamnatin da ‘yan majalisu SERAP ta ce wajibi ne gwamnati ta jinkirta bai wa jihohi kudaden har sai bayan an rantsar da sabuwar gwamnati.