Connect with us

Labarai

Yemi Osibanjo ya jagoranci taron majalisar zartaswa yau

Published

on

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartaswa a fadar shugabacin kasa ta Villa da ke Abuja.
An dai fara gudanar da taron ne da misalin karfe goma na safiyar yau, inda aka bude shi da taken Najeriya.

Bayan nan ne kuma ministan albarkatun ruwa Sulaiman Adamu ya gabatar da addu’a a bangaren musulmi yayin da ministan Naija Delta ya gabatar da addu’a a bangaren mabiya addinin kirista.

A al’adance dai akan gudanar da taron ne a kowacce laraba sai dai na yau litinin na zaman taron na karshe kasancewar wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari na farko na gab da karewa.
A ranar 29 ga watan da muke ciki na Mayu ne za’a rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a baya-bayan nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!