Labarai
NLC ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako guda wajen mayar da kudin ma’aikata da aka karkatar

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako guda domin mayar da kudaden ma’aikata da ake zargin an karkatar daga Asusun Inshorar Ma’aikata, tare da bukatar a gaggauta kafa Hukumar Gudanarwar Asusun Fansho na Ƙasa PENCOM.
A wata sanarwa da aka fitar bayan taron Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa da ya gudana a Abuja, NLC ta yi gargaɗi cewa idan gwamnati ta gaza cika waɗannan buƙatu, a shirye kungiyar take domin tsindima yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar nan
Taron wanda Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya jagoranta, ya tattauna muhimman batutuwa da ke shafar ma’aikata, ƙungiyoyin kwadago, da halin da ƙasar ke ciki.
You must be logged in to post a comment Login