Labarai
NLC ta bai wa gwamnatin tarraya makonni ta kawo ƙarshen matsalarta da ASUU

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta bai wa gwamnatin tarraya wa’adin makonni huɗu ta kawo ƙarshen matsalar da ke tsakaninta da ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU da sauran ƙungiyoyin manyan makarantun ƙasar.
Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai.
Joe Ajaero, ya ce, da zarar mako huɗu ya cika, kuma ba su ga wani mataki da aka ɗauka ba, to NLC din za ta ɗauki matakin da duk wani ma’aikaci da duk wata ƙungiya za ta shiga maganar har sai an samar da mafita.
Haka kuma, shugaban ƙungiyar ta NLC, ya kara da cewa, a halin yanzu an wuce lokacin da za a riƙa yi wa ƙungiyoyi barazana.
You must be logged in to post a comment Login