Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

NNPC da DPR ne ke taimakawa wajen fasa-kwaurin man fetur – Hamid Ali

Published

on

Shugaban hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, Kanal Hamid Ibrahim Ali ya alakanta matsalar yawan fasakwaurin man fetur zuwa kasashen ketare da gazawar kamfanin man fetur na NNPC da sashin albarkatun man fetur na kasa.

Hamid Ali ya dai zargi bangarorin biyu da rashin kiyaye dokokin da aka shimfida wajen magance matsalolin fasakwaurin man fetur a Najeriya.

Ya ce kamfanin na NNPC na ci gaba da ba wa gidajen man da su ke kusa da iyakokin kasa man fetur wanda hakan ya saba wa shawarwarin hukumar.

Ya kuma zargi sashin albarkatun mai, DPR, da ci gaba da sahale gina gidajen man a iyakokin kasar nan, yayin da hakan yasabawa doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!