Connect with us

Labarai

NNPC:ya biya abokan huldansa kudaden ariya dala biliyan daya da rabi

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC ya biya abokan huldar sa wato manyan kamfanonin mai na kasa da kasa kudaden ariya dala biliyan daya da rabi.

 

Rahotanni sun ce kamfanonin suna bin kamfanin na NNPC ariyar dala biliyan biyar da miliyan dari daya.

 

Shugaban kamfanin na NNPC Maikanti Baru ne ya bayyana haka yayin wani taron masana kan tattalin arzikin makama shi karo na goma sha biyu da ke gudana a Abuja.

 

Ya ce kudaden wani bangare ne na hadaka da kamfanin na NNPC ke yi da takwakarorin sa manyan kamfanonin mai na kasa da kasa wajen harkokin mai a Najeriya.

 

Maikanti Baru ya kuma ce NNPC na aiki dare ba rana don ganin an samu nasarar wajen fadada ayyukan su da nufin cin riba mai yawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!