Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar Yan sanda ta damke wata mace da ake zargin ta sa wa mijinta shinkafar bera a abinci

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kano ta damke wata mata mai shekaru goma sha biyar mai suna Hasana Lawan dake kauyen Bechi a karamar hukumar Kumbotso bisa zargin sanyawa mijinta shinkafar bera a cikin abinci.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan DSP Abdullahi Haruna ne ya tabbatar da kama matar cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya Talata.

 

Abdullahi Haruna ya ce tun a ranar 16 ga watan Afrilun da muke ciki, rundunar yan sandan ta karbi rahoton cewar matar ta baiwa mijinta shinkafar bera a cikin abinci.

 

A cewar sa jim kadan bayan da ya ci abincin ne aka dauke shi ranga-ranga zuwa Asibitin Murtala da ke nan Kano domin nema masa magani

 

Ya kuma ce tuni rundunar ta fara bincike kan al’aamrin kuma da zarar sun kammala za su aike da wacce ake zargin gaban kuliya domin ta girbi abin da ta shuka.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!