Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nura M. Inuwa ya nemi afuwar masoyan sa

Published

on

Mawaƙin nan Nura M. Inuwa ya nemi afuwar masoyan sa kan rashin cika alƙawarin da ya yi musu na sakin sabon kudin waƙoƙin sa.

Ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Nuran ya roƙi masoyan sa kan su yi masa afuwa, sannan su ƙara haƙuri zai saki kundin waƙoƙin nan ba da jimawa ba.

Hakika na sa’ba muku akan rashin sani, na kuma fahimci shiru baza ta gamsar da ku ba, na so ace shirun da nayi yazo da…

Posted by Nura M inuwa on Sunday, March 7, 2021

 

A baya dai mawaƙin ya yi alƙawarin cewa zai saki kundin waƙoƙin sa na wannan shekara a ƙarshen watan Fabrairun da ya shuɗe.

Bisa al’ada dai dai Nura M. Inuwa yana fitar da kundin waƙoƙin sa sau biyu a kowace shekara.

Amma a shekarar 2020 da ta gabata bai fitar da kundin ba, lamarin da ya sanya masoyan sa suka riƙa neman ba’asi.

A zantawar sa da Freedom Radio, Nuran ya ce, abin da ya sa bai fitar da kundin waƙoƙi a 2020 ba, shi ne domin ya bai wa wasu dama.

Yanzu haka dai dubunnan al’umma ne suka shiga yin tsokaci tare da bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan neman afuwar da mawaƙin ya yi a kafafen sada zumunta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!