Labarai
NYCN ta bukaci a samar da dokoki kan hana biyan kuɗin fansa

Kungiyar Matasa ta Arewacin kasar nan NYCN ta bukaci hukumomin tsaro da su haramta tare da samar da dokoki kan hana biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, tana cewa hakan ne kawai zai kawo ƙarshen garkuwa da mutane a Najeriya.
Ta cikin wata wasika da ya aike zuwa ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Shugaban kungiyar matasan, Isah Abubakar, ya bayyana cewa biyan fansa na ba ‘yan bindiga ƙarfi da kuɗin sayen makamai.
Kungiyar ta ce daukar wannan mataki zai taimaka wajen yaki da masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login