Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

ONDO:yan fashi da makami sun kashe mutane bakwai a garin Ido-ani

Published

on

Wasu ‘yan fanshi da makami sun kashe mutane bakwai a wani bankin kasuwanci da ke garin Ido-ani a yankin karamar hukumar Ose a jihar Ondo.

 

Rahotanni sun ce ‘yan fashin sun kai hari bankin ne da misalin karfe goma sha biyu na ranar jiya litinin.

 

Shaidun gani da ido sun ce biyar daga cikin wadanda suka rasa rayukansu ma’aikatan bankin ne da kuma wani mataimakin principan na wata babbar makarantar Sakandire da ke yankin da kuma jami’in dan sanda daya.

 

Haka zalika bayanai sun tabbatar da cewa ‘yan fashi da makamin sun sace kudade masu tarin yawa sannan sun dau tsawon kusan awa daya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!