Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Taraba:Mutane goma sun rasa rayukansu sakamakon rikici kabilanci

Published

on

Shugaban karamar hukumar Wukari a jihar Taraba Mr. Daniel Adi, ya ce, mutane goma sun rasa rayukansu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin kabilun Tivi da Jukun.

 

Ya ce ba ya ga wadanda suka rasa rayukan su, wasu mutanen da dama sun samu munanan raunuka sanadiyar rikicin.

 

Da ya ke zantawa da manema labarai jiya a garin Wukari, Mr Daniel Adi, ya ce; rikicin ya shafi sama da kauyuka tara a yankin mazabar Kente da ke karamar hukumar ta Wukari.

 

Mr Daniel Adi, ya kuma ce ko a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, gidaje da dama tare da makarantar sakandire ta gwamnati da ke Kente suna can suna ci da wuta sakamakon banka wuta da ‘yan tarzoma su ka yi.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Taraba David Mishal, ya tabbatar da faruwar lamarin

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!