Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Otel -Otel na jihar Kano na gudana babu izinin Gwamnati

Published

on

Otel dake jihar Kano wadanda baki ke sauka daga gurare da da dama suna tafiyar da harkokin su ne ba da izinin hukuma ba.

Manajan Daraktan hukumar yawan shakatawa ta jihar Kano Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyan Freedom.

Yusuf Lajawa yace tun kafa hukumar ta kula da sha’anonin shakatawa ta jihar Kano a shekarar 1994 bata yin aikinta yadda ya kamata  sakamakon ko in kula da shugabannin baya suka yi wa hukumar ta yawan shakatawa.

Gwamnatin Kano ta ware fiye da Naira biliyan biyu domin gina asibitoci a sababbin masarautu

Dangote ya tallafa mana da kayayyakin aiki-‘Yan bijilanti na Kano

Yusuf Lajawa ya kara da cewa hukumar tasu na kula da bangarori na yau da kullum da suka hada da masu yiwa mutane hanyar tafiye tafiye da  sauran su da kuma dakunan cin abinci.

Haka guraran bukukuwa da ake kira da Event centres na daya daga cikin bangarori da hukumar ta yawan shakatawa ke lura da su

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!