Connect with us

Labarai

Amarya ta rasu ana dab da bikinta

Published

on

Wata matashiyar amarya mai suna Atika Isah yar asalin unguwar Sunusi dake jihar Kaduna ta rasa ranta a yayin da ake dab da fara shirye-shiryen bikin aurenta.

Ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki ne aka sanya domin daura auren marigayiyar da angonta mai suna Engr. Nura Yahuza, kamar yadda kuke gani a katin daurin auren dake kasa.

Sai dai cikin ikon Allah amaryar ta rasa ranta sakamakon gajeruwar rashin lafiya a daren jiya Lahadi.

Shima a nasa bangaren angon ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa

 

Tuni dai akayi jana’izar marigayiyar kamar yadda musulunci ya tanada a masallacin jumu’a na Usman Dan Fodiyo dake unguwar Sanusi a jihar Kaduna.

Idan zaku iya tunawa dai ko a karshen shekarar da ta gabata wata amarya ta rasa ranta, a yayin da take tsaka da rabon katin bikinta, sanadiyyar hatsari a babur mai kafa uku wato a dai-daita sahu (Napep) sakamakon ruwan sama da aka tafka a unguwar Rigasa dake jihar ta Kaduna.

Kazalika a watan Disamba na shekarar 2019 da ta gabata wata amarya ta rasa ranta, sakamakon fadawa rijiya a rashin sani, yayin da ake tsaka da shagalin bikinta a karamar hukumar Danbatta dake nan Kano.

Labarai masu alaka:

Amarya ta haihu bayan wata hudu da Aure

Garin da ake aure akan naira dubu hamsin (N50,000) kacal a Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!