Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

PDP ta caccaki Buhari kan shirin daga likafar Magu

Published

on

Jam’iyyar PDP ta yi All- wadai kan shirin da tace fadar shugaban kasa na yi na bawa tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasa EFCC Ibrahim Magu sabon mukami.

A cewar jam’iyyar, ana zargin Magu da aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa a lokacin da yake rike da mukamin hukumar ta EFCC.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun Jam’iyyar ta PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya sanya wa hannu a ka kuma raba ga manema labarai yau a Abuja.

Sanarwar ta ce, bai kamata ba ace gwamnatin kasar nan dake ikirarin yaki da cin hanci da rashawa kuma ta goyi bayan cin hancin.

Sanarwar ta kuma ce, gwamnatin shugaba Muhammad Buhari na shirin nada Ibrahim Magun ne mukamin mataimakin Sufeto Janar na ’yan sandan kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!