Connect with us

Labarai

PDP ta dage taron kwamitin zartaswarta na ƙasa karo na 99

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP, ta sanar da dage taron kwamitin zartaswarta na ƙasa karo na 99, wanda aka shirya gudanarwa ranar Talata, 27 ga watan nan da muke ciki na Mayu, a shalkwatar jam’iyyar da ke birnin tarayya Abuja.

 

Sanarwar dage taron na kunshe ne ta cikin wata takarda da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fitar a ranar Lahdi.

 

A cewar sanarwar, PDP ta yanke shawarar dage taron ne domin bai wa kwamitin sulhu karkashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, damar ci gaba da aikinsa na hada kan ’ya’yan jam’iyyar tare da warware sabanin da ke damunta.

 

Jam’iyyar ta ce, za a fitar da sabuwar ranar taron daga baya, a bisa tanadin kundin tsarin mulkinta na sheakarar 2017 wanda aka yi wa kwaskwarima, da kuma Sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2022.

 

Tuni dai PDP ta bukaci mambobinta da su kasance cikin shiri, tare da bin duk wasu umarni da za su biyo baya daga shugabancin jam’iyyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!