Labarai
PDP ta daukaka kara kan umarnin kotu na kamo Tanimu Turaki SAN

Wani tsagi na jam’iyyar PDP, ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki SAN, ya ɗaukaka ƙara kan umarnin kotu da ya ba da izinin kama shi.
Turaki ya bayyana wannan umarni na kotun koli a matsayin wanda bai dace ba, inda ya ce an yi masa rashin adalci, tare da neman a soke wannan mataki nan take.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin cikin gida na PDP na ci gaba da ɗaukar sabon salo, yayin da bangarori daban-daban ke fafatawa kan shugabanci da ikon tafiyar da jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login