Connect with us

Labarai

Pi-CNG ya nuna damuwa kan rahotannin da suka bayyana kan fashewar mota a Kaduna

Published

on

Shirin Shugaban Kasa kan Daskarariya Iskar Gas da kuma abubuwan hawa masu amfani da  Lantarki Pi-CNG & EV ya nuna damuwa kan rahotannin da suka bayyana kan fashewar wani abu a wata mota a safiyar jiya Lahadi a jihar Kaduna.

 

Ta cikin wata sanarwa da Shugaban, Sashen Harkokin Sadarwa na ma’aikatar Onyekachi Eke, ya fitar aka rabawa manema labarai, ta ce  halin yanzu, babu tabbacin sanadin faruwar lamarin, yayin da bincike ke ci gaba da gudana.

 

Sanarwar ta kara da cewa shirin na aiki kafada da kafada da hukumomin jihohi da na tarayya don tabbatar da gaskiyar lamarin.

 

Hukumar ta ce CNG makamashi ne mai aminci, abin dogaro, kuma mai araha, tare da fa’idar rage gurbatar iska da tallafawa makamashi mai tsafta, da ta bukaci jama’a da su zauna lafiya, tare da watsi da jita-jita ko rahotanni masu tayar da hankali  yayin da bincike ke gudana.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!