Labarai
Prime College ta musanta amincewa da sasanci kan rikicin rufe Makarantar

Makarantar Prime College da ke Kano ta musanta cewa ta amince da sasanci a wajen kotu domin sake buɗe makarantar bayan taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Hukumar kula da Makarantu masu zaman kansu da kuma malaman sa-kai ta jihar KSPVIB.
A wata sanarwa da lauyoyin makarantar suka fitar, da yammacin yau Asabar, sun bayyana cewa sun yi mamaki kan wani rahoton da ya fito a kafafen yaɗa labarai da ke nuna cewa wai an cimma yarjejeniya tsakanin makarantar da hukumar, alhali babu wani umarnin kotu da ta taba rufe makarantar.
Sanarwar da lauya Femi Sunmonu ya sanya wa hannu ta ce: “Prime College ba ta amince da kowace irin yarjejeniya ta wajen kotu ba. Idan za a yi wani sasanci, sai dai ta hanyar gaskiya da bin ƙa’ida tare da halartar lauyoyi da wakilan makarantar.”
Haka kuma sanarwar ta lauyan Prime College ta ƙara da cewa, duk da cewar rufe makarantar ya kawo cikas ga ɗalibai, amma ba za ta lamunci a tauye haƙƙinta ba, domin za ta ci gaba da neman adalci a gaban kotu.
Idan za a iya tunawa, rikicin ya fara ne bayan makarantar ta sanar da sabon tsarin kuɗin makaranta a shekarar karatu ta 2025/2026, inda ta danganta ƙarin da hauhawar farashi da kuma bukatar inganta ilimi. Sai dai, ƙalilan daga cikin iyaye ƙasa da 20 suka ƙi amincewa da sabon tsarin, suka kai ƙorafi ga hukumar ta PVIB.
Daga bisani sakataren hukumar ta PVIB, Malam Baba Abubakar Umar, ya kafa kwamiti na wucin gadi da ya ƙunshi iyaye da malamai, inda yawancin su suka goyi bayan ƙarin kuɗin.
Amma hukumar ta ce tattaunawar bata kammala ba, sannan ta bayar da umarnin a janye ƙarin.
Prime College ta koka da cewa duk ƙoƙarinta na sasanta matsalar da hukumar PVIB ya ci tura, sai dai cin mutunci da tozarci.
Makarantar ta kuma ce, ta na ci gaba da neman adalci a gaban kotu tare da jaddada cewa dakatar da karatun yara marasa laifi, ko na kwana ɗaya ne, ba adalci ba ne.
You must be logged in to post a comment Login