Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Rahoto: ƴan kasuwa sun zargi kamfanoni da ɓoye kaya har sai sun yi tsada

Published

on

Ƴan kasuwar Dawanau a nan Kano sun alaƙanta tashin farashin kayan masarufi da yadda masana’antu da manyan ƴan kasuwa ke saye kaya su ɓoye har sai yayi tsada.

Koken na su na zuwa ne adaidai lokacin da al’umma ke bayyana damuwa kan yawaitar tashin farashi a kasuwa.

A ziyara da muka kai kasuwar ta dawanau mun ga yadda ake lodin kaya a cikin manyan motocin dakon kaya, inda a wani bangare kuwa shaguna cike da masara da aka ajiye.

Sai dai musu sayar da wannan kaya sun bayyana cewa a yanzu kamata yayi ace kayan abinci farashin su ya sakko domin kuwa na damina sun fara zuwa amma sakamakon yadda mutane ke ɓoyewa ya sanya duk suka yi tsada kuma farashin ke karuwa a kullum.

Ɗan kasuwa Malam Idris ya ce “Mu ƴan kasuwa ba mu ne muke da hurumin tayar da farashi ba, domin kuwa muma sarowa uke daga masana’antu ko kamfanoni, don haka kowanne ɗan kasuwa idan ya sayo kaya yana buƙatar samun riba”.

Shi kuwa Ibrahim Hamza cewa yayi “Ya ce, kowanne ɗan kasuwa na da burin sauƙakawa al’ummar su, sai dai babu yadda za mu yi domin kuwa muna son samun riba a kasuwancin wanda hakan ne ya sa mutane suke ganin mu muke tsawwalawa”.

 

Al’umma na kokawa kan yadda a kullum ake samun yawaitar tashin farashin kayayyaki musamman ma kayan abinci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!