Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shaikh Jafar Mahmud Adam ya cika Shekaru 16 da rasuwa

Published

on

A yau Alhamis ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Sheikh Jafar Mahmud Adam, ya cika shekara 16 da rasuwa.

Malamin ya rasu ne bayan da wadansu da ake zargi ‘yan bindiga ne suka harbe shi,lokacin da yake jagorantar Sallar Asuba a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 a nan Kano.

An haifi Marigayi Shaikh Jafar Mahmud Adam a ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a garin Daura da ke jihar Katsina.

Ya kuma dawo Kano ne don yin karatun allo yana da kimanin shekara hudu a duniya a hannun yayarsa, inda kuma ya samu nasarar haddace Al-Kur’ani mai girma a shekarar 1978.

Shaikh Jafar Mahmud ya fara karatun boko a shekarar 1990, daga bisani kuma ya yi karatun addinin Musulunci a kasashen Saudiyya da Sudan, inda ya samu digiri na biyu.

Malamin yana komawa garin Maiduguri duk shekara don gudanar da tafsirin Alkur’ani a watan azumin Ramadan.

Marigayi Shiekh Jafar Mahmud Adam ya kwashe shekaru da dama yana bawa addinin musulunci gudunmawa ta hanyar karantar da al’umma da yin tafsirai dakarantar da manyan littattafai a sassan arewacin kasar nan dama kasa baki daya.

A wata safiyar ranar Talata ne wasu da akke kyautata zaton yan bindiga ne suka harbe heikh Jafar Mahmud Adam inda suka kashe shi har lahira lokacin da yake jagorantar sallar Asuba a masallacin Almuntada dake Dorayi a nan  Kano.

Sai dai kuma har ya zuwa yanzu dai marigayin yayi tsayin shekaru 16 da rasuwa al’umma musulmai na cigaba da jin radadin mutuwarsa.

Malam Abdulwahab Abdallah limamin masallacin Gadon Kaya dake nan Kano, guda ne daga cikin malaman da Shiekh Jafar ya yi karatu a hannunsu, ya bayyana cewa ‘har ya zuwa yanzu ba’a cike gibin daya bari ba’.

A hannu guda daya daga cikin ‘ya’yan Malamin a nan Kano Malama Zainab Jafar Mahmud ta ce mahaifin nasu babban jigo ne ga rayuwarsu, dama ta al’umma baki daya, wanda kuma ya zamo babban jigon da baza’a iya samun sa ba a yanzu’.

Rahotanni dai sun nuni cewa har ya zuwa yanzu ba’akai ga gano wadanda suka kashe shekik Jafar Mahmud ba.

Rahoton: Shamsiyya Farouk Bello

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!