Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

RAHOTO: Ranar yada labarai don ci gaba ta duniya

Published

on

Ranar yada labarai don ci gaba ta duniya, rana ce da ke mayar da hankali wajen fito da dabarun fitar da bayanai ta hanyar jin ra’ayoyin al’umma musamman ma matasa.

A wani babban taro na zauren majalisar dinkin duniya a shekarar 1972 aka ware duk ranar 24 ga watan kowacce shekara a matsayin ranar yada labarai don ci gaba wajen fitar da bayana.

Tun da fari dai zauren majalisar dinkin duniya ne ya yanke hukuncin ware duk ranar 4 ga watan oktoban kowace shekara a matsayin ranar yada labarai don ci gaba inda ranar ta dace da ranar bikin majalisar dinkin duniya.

Sai dai zauren majalisar dinkin duniya na sabunta dabarun bunkasa fasahar sadarwa fitar da bayanai duk bayan shekara 10 da nufin fito da sabbin dabaru tare da amincewa da fitar da bayanai ta hanyoyin sadarwa na magance matsaloli tare da fayyace gaskiya a fadin duniya.

Masana na ganin cewa yawaitar hanyoyin samar da bayanai na hada kan al’umma tare da bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da talauci, kamar yadda a wannan lokaci da duniya ke fama da annobar corona.

Al’umma dai na ganin matukar gwamnatin na fitar da bayanai ga al’ummar ta to kuwa za a fahimci inda ta sanya gaba, tare da kara tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Dr Sulaiman Yar adu’a Malami ne a tsangayar koyar da aikin jarida a jami’ar Bayero da ken an Kano, ya ce ranar na baiwa al’umma damar tattaunawa da shugabannin su tare da sama da hanyoyin ci gaban su.

Yana mai cewa fasahar sadarwa wajen fitar da bayanai na taimaka al’umma sanin abubuwan da gwamnati ke aiwatarwa na ci gaban su.

Taken bikin ranar ta bana shi ne: sanin muhimmancin tarihi da fasahar sadarwa wajen fitar da bayanai.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!