Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Rahoto : Wasu mata sun rasa rayukan su wajen siyayyar auren ‘Yar su a Kano

Published

on

A Safiyar jiya Asabar ne aka tashi da ruwan sama a jihar Kano wanda ya yi sanadiyyar rushewar wata rumfa a kasuwar Kurmi inda wasu mata da suka zo nan Kano domin karasa siyayyar kayan auren ‘yar su da za’ayi a yau hahadi suka rasa rayukan su.

Matan dai da suka rasa rayukansu sun taso ne daga garin Funtuwa ta jihar Katsina su uku da nufin siyan ragowar kayan auren ‘yar su wanda ba su yi ba.

Sai dai a zantawar da freedom a da guda daga cikin matan da suka zo Kanon domin karasa siyayyar ta ce tabar wadanda suka rasun a baya ita da wanda zai musu rakiya zuwa shagon da zasu siyayyar suna gaba taji karar faduwar ginin da ya danne su juyowar ta keda wuya ta ga akan ‘yan uwanta abun ya faru.

“Ta ce sun gama siyayyar su ka kwari sai suka ce bari su zo kurmi domin karasa siyayyar a raine zaiyi halin sa”.

Salisu Dan Dume shine  direban da ya dauko su daga Funtuwa ya ce sun kawo kayansu wajan motar da nufin komawa gida sai suka shida masa cewa sun yi mantuwa zasu koma cikin kasuwar inda suka ajiye kayan da suka sayo suka koma kasuwar wanda yaji sun dade ya kira wayar dayar sai ya ji labarin abunda ya faru.

Abdullahi Mai Kano shine sarkin kasuwar Kurmi ya ce rashin ingancin ginin da aka yiwa shagon ne ya sanya shi faduwa.

“Ya ce kasuwar na kusa da kwatar Jakara wanda gurin ba shida kwari domin tamkar kogi ne”.

Suma wasu mazauna kasuwar sun ce ana tsaka da ginin ne abun ya faru wanda matan suka zo hucewa sai dai dama sun shidawa sarkin kasuwar Kurmi halin da ake ciki cewar ginin da ake zai haifar da Matsala a kasuwar.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara da ta ziyarci kasuwar ta ce yan kasuwar sun dade suna kokawa kan gine ginen kasuwar da magudanan ruwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!