Rahotonni
Rahoto: yadda bikin ranar zaman lafiya ta duniya ya kasance a ƙasar nan
A ranar 21 daya ga watan Satumbar kowacce shekara rana ce da majalisar ɗunkin duniya ta ware a matsayin ranar zaman lafiya.
Ranar na mayar da hankali wajen kawo mafita kan tashe tashen hankula a ke fama dashi na banbancin addini yare da kuma kabilai a fadin duniya
Sai dai binkin a bana yazo lokacin da ake fama da matsalar rashin tsaro a sassan ƙasar nan musamman na harin ƴan bindiga da garkuwa da mutane.
A wani Rahotan da wata cibiyar tsaro a kasar nan ta fitar ya yi nuni da cewa a watan satumba rashin tsaro yayi nuni sama da watan Agustan da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa ayyukan ta’addanci yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 688 a fadin ƙasar nan.
Sai dai masana na kalon tasirin rashin zaman lafiya da rashin daukar mataki da ya dace da Kuma biyan kudin fansa da ma rashin aikin yi da illimi ga matasan kasar nan ne ya haifar da tsanantar matsalar.
Masanan sun ce idan har ana son dorewar zaman lafiya sai an gyara zukatan matasa, da sa musu san Allah da manzon rahma a ko da yaushe .
Sannan a hada kai da kuma kaunar juna da yin yafiya a tsakanin Al’umma.
You must be logged in to post a comment Login