Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Rahoto: yadda iskar Gas ke tsada

Published

on

Masu gudanar da sana’ar ɗura iskar gas na kokawa kan yadda ake samun tashin farashin sa, lamarin da ke sanya masu saye don amfanin gida cikin wani yanayi.

Tuni dai al’umma ke kokawa kan yadda iskar gas ta yi tsada, kasancewar a yanzu an fi mayar da hankali wajen yin amfani da shi a wajen girki a gidaje.

A zantawar mu da mai sana’ar ɗura iskar gas a unguwar Sharaɗa da ke Kano Malam Bashir Abdullahi ya ce gas yayi tsada sosai fiye da tunanin mutane.

“Za ki ga mutum ya zo da 12.5 a da a cika masa a kan farashin N2700 yanzu ya kai kimanin farashin N7000, to ina abin dadi a wannan rayuwa, ta yadda a yanzu mutum zai zo ma a kan cewar bashi da kuɗi a zuba mai N1000 ko kuma na N1500 sai an yi albashi zai biya”.

Bashir Abdullahi ya kuma ce “gas a sharaɗa muna siyan 50kg akan kudi N10, 000 wani lokacin kuma N9500 har ta kai ga cewa ya ninka kuɗinsa yanzu zuwa N20,000 ko kuma N25,000 a hakan ma an baka sari na kamfani”.

“Nawa za ka bawa mai mashin ɗin da ya yo maka dako wanda aƙalla kowanne guda ɗaya ana bada N400 ne a hakan ma idan mutum ya je da kansa ba lallai ne ya hada N25, 000 ɗin ba” in ji Abdullahi.

Tashin farashin iskar gas ɗin dai na da nasaba da yadda farashin dala ke ƙara tashi a ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!