Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

2022 World Cup: ‘Yan wasan Super Eagles sun gudanar da atisaye na farko

Published

on

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles sun gudanar da daukar horo na farko a ranar Talata 05 ga Oktoban 2021 da muke ciki a filin wasa na Teslim Balogun dake Lagos.

Wannnan dai na zuwa ne gabani wasan da tawagar zata buga a ranar Alhamis mai zuwa da kasar Afrika ta tsakiya a wasan neman tikitin buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 a Qatar.

Sansanin da ake saran halartar ‘yan wasa 22 da zasu cigaba da daukar horo domin tunkarar wasan

Wanda mai horar da kungiyar Gernot Rohr ya jagoranta da mataimakinsa Joseph Yobo da Nabil Trabelsi da kuma Jean Luc Royer.

Yayinda mai horar da masu tsaran raga Alloy Agu ya halarci sansanin bayan horas da masu tsaran raga Daniel Akpeyi da Francis Uzoho da ya yi.

Kawo yanzu sansanin na Super Eagles ya samu halartar ‘yan wasa 21 ciki har da Osimhen, Iheanacho da kuma Omeruo.

Sai dai mai tsaron gida na Sparta Rotterdam Maduka Okoye ne bai halarci sansanin ba, amma tuni ‘yan wasan suka kammala daukar horon a sansanin ake sa ran rufewa a ranar Larabar nan.

‘Yan wasan da kawo yanzu suke a sansanin sun hada da  Ejuke Chidera, Daniel Akpeyi, Onuachu Paul, Samuel Kalu, Kevin Akpoguma, Jamilu Collins, Innocent Bonke, Chidozie Awaziem, Taiwo Awoniyi, William Ekong, Frank Onyeka.

Sai Leon Balogun, Joseph Aribo, Calvin Bassey, Ola Aina, Ahmed Musa, Shehu Abdullahi.

Sauran sun hada da Francis Uzoho, Kenneth Omeruo, Victor Osimhen, Kelechi Iheanacho, Moses Simon.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!