Rahotonni
Rahoto : Yadda tsadar rayuwa ta jefa ‘yan Najeriya cikin kunci
Daga Shamsiyya Farouk Bello
Masana kan tattalin arziki sun bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu tattalin arzikin kasar nan bai hau kan farkin gyaruwa ba, duba da cewa gwamnati bata hau kan turbar data dace ta farfado da tattalin arziki.
haka zalika masana sun kara da cewa, sun bayyana cewa al’ummar kasar nan suna cikin matsakaicin talauci, hakan tasa suka kara shiga cikin matsin rayuwar da suke ciki a yanzu.
Mazauna kasar nan dai na kokawa dangane da matsin tattalin arzikin da kasar nan yake fama dashi.
Ta inda al’umma da dama da ada suke cin abinci sau uku, daga bisani kuma ya dawo ci sau biyu, yayin da wadanda suke ci sau biyu suka dawo sau daya abun da ake kira da tazarce , wasu kuwa sai su yini, su kwana basu ga ko kanzo ba.
A gefe daya kuwa ‘yan kasuwa na kokawa kan rashin kasuwa kasancewar idan sun kasa kayayyaki ba ko yaushe suke samu masu siya ba, yadda wataran sai su yini ko sisin koabo ba siyi ba.
Wasu mutane da Gidan Radio Freedom ta tattauna dasu sun bayyana halin da suke ciki a yanzu.
“Lamarin babu dadi a gaskiya kasancewar babu ci da sha a yanzu mu talaka muke shan wuya”.
“Ka zalika muna fuskanta matsala sosai kasancewar an kara kudin komai a yanzu”
Hakan tasa gidan Radio Freedom ta tattauna da wani masanin tattalin arziki a Jami’ar Yusuf Maitama sule dake nan Kano Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata kan mai ya sababa tsadar rayuwa a wannan lokacin ya yin da yake cewa idan har gwamnatin kasar nan na san shawo kan wannan matsalar to shakka babu sai ta tuntubi shawararin masana kan harkokin tattalin arzikin.
A hannu guda kuma mutane na kokawa kan yadda Najeriya zata cika shekarun 60 da samun ‘yan cin kai a tafarkin dumukuraddiyya amma kawo yanzu bai ci ribar dumukuradiyyar ba, akan haka ne muka tuntube masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge mai yasa talaka ke shan wuya a wannan lokacin
Farfesan ya kara da cewa,ba wanda ya cancanci ya sha romon damukradiya kamar talaka, duba da cewa su suke jefawa shugabanni kuri’a har su samu su dare kujerar mulki, don haka talaka bai can-canci ya samu kansa a ukubar da yake ciki a yanzu ba.
You must be logged in to post a comment Login