Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashawa: Kwanaki 68 da bankado yiwa malamai fince a Kano, ina aka kwana?

Published

on

Kwanaki 68 kenan da bankaɗo badaƙalar zaftare kuɗin addu’a ga malaman addini da gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya basu.

Freedom Radio ce dai ta bankaɗo zargin da wasu malamai suka yi na cewar mai baiwa gwamnan Kano shawara kan addini Ali Baba Agama Lafiya Fagge, da ɗansa Huzaifa Ali Baba sun zaftare musu kuɗinsu.

Kuma bayan fadada bincike hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta karɓo kuɗaɗen tare da mayar wa malaman.

Sai dai har kawo wannan lokaci hukumar ba ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu ba, lamarin da ke jefa shakku a zukatan al’umma kan yaƙi da rashawar.

A baya-bayan nan dai gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce jihar Kano ce ke kan gaba wajen yaƙi da rashawa.

Auwal Musa Rafsan Jani, babban jami’in ƙungiyar Transparency International ya shaida wa wakiliyarmu Shamsiyya Haruna cewa, yaƙi da rashawa a Najeriya har yanzu bai samu wani sauyi ba.

Yace a baya an sanya ran cewa za a yaki cin hanci da rashawa da gaske, sai dai alamu na nuna cewa babu wani abu da ya sauya musamman rashin bin dokoki da tsari wajen hukunta wadanda aka kama da laifi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!