Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Siyasa

Rashin lafiya ta hana Sanata Dino Melaye halartar zaman kotu

Published

on

Sanata mai wakiltar yammacin Kogi Dino Melaye bai halacci zaman kotu ba a yau.

Sanata Dino Melaye dai yana fuskantar tuhuma ne sakamakon mallakar bindigu ba bisa kaida ba amma duk da haka lauyoyin dino Melaye sunce bashi da lafiya.

Amma wasu mutane biyu da ake zargi tare da Dino Melaye Kabir Saidu wanda aka fi sani da Osama da Nuhu Salihu wanda ake kira da suna Smally  sun halacci zaman kotun na yau domin amsa tuhume tuhumen da ake yi musu.

Lauyoyi masu kare Dino Melaye Barrister Yemi Muhammad wanda ya wakilci Chief Mike Ozekome yace Sanata Dino Melaye bai halacci zaman kotun ba saboda bashi da lafiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!