Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Rashin maye gurbin ma’aikatan da suka yi ritaya ke ta’azzara rashin aikin yi – Dr. Abdurrazak

Published

on

Daga Mu’azu Tasi’u Abdurrahaman 

Wani masanin tattalin arziki a Jami’ar Yusif Maitama Sule a nan Kano ya bayyana cewa rashin maye gurbin ma’aikatan da suka yi ritaya na taka rawa wajen ta’azzarar rashin aikin yi a kasar nan.

Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge ne ya bayyana haka ta cikin shirin Duniyarmu A Yau na nan Freedom Radio da ya mayar da hankali kan yawaitar rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar nan.

Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge, ya ce, “A mafi yawan lokuta ka’idojin da gwamnatoci da kuma sauran kamfanoni ke shimfidawa masu neman aikin na taimakawa wajen yawaitar marasa aikin yi a kasar nan, a saboda haka akwai bukatar mahukunta su yi gyaran fuska tare da samar da dokoki da kuma saukakakken sikelin da ake dubawa kafin daukar ma’aikata”.

A nasa bangaren wakilin ‘yan kasuwa a cikin shirin Alhaji Shitu Sani Marshal cewa yayi, tsauraren matakai da hukumomin dake bai wa ‘yan kasuwa bashi suke shimfidawa na daga cikin matsalar dake kara haifar da rashin aikin yi a kasar nan.

Ya ce, “A halin da ake ciki akwai bukatar gwamnatocin jahohi da na tarayyar kasar nan su rungumi yan kasuwa ta hanyar ba su saukakakken bashin da zai taimaka musu wajen fadada kasuwancinsu”.

Shi ma Mal Sadiq Abubakar Sadiq da ya kasance a cikin shirin ya bayyana cewa ‘yan siyasa sun taimaka wajen ta’azzarar matsalar rashin aikin yi a kasar nan ta hanyar alkawartawa al’ummarsu samar musu gwaggwaban aiki a gwamnati, wanda hakan ya taimaka wajen sanya mutuwar zuciya ga matasan kasar nan musamman ‘yan boko.

Wakilin mu Mu’azu Tasi’u Abdurrahaman ya ruwaito cewa, bakin dai sun yi kira ga al’ummar kasar nan musamman matasa da su tashi tsaye wajen kirkirar Sana’o’i domin dogaro da kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!