Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Karin kuɗin lantarki: Kamfanoni za su rage ma’aikata a Kano

Published

on

Ƙungiyar masu kamfanoni a unguwannin Bompai da Tokarawa ta ce, akwai yiwuwar ta rage ma’aikata a kamfanunuwan sakamakon ƙarin farashin wutar lantarki.

Shugaban ƙungiyar masu masana’antu a unguwar Alhaji Sani Sule ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Duniyarmu a yau na nan Freedom Radio a ranar Litinin, wanda ya mayar da hankali kan ƙarin kuɗin lantarki.

Alhaji Sani Sule ya ce, zaɓi biyu ne ya rage musu, shi ne su yi ƙarin farashi kan kayayyakin da suke samarwa, wanda hakan zai kawo musu ƙarancin masu sayen kayansu, a don haka tilas su rage ma’aikatan su domin samun damar ci gaba da gudanar da kamfanunuwansu.

A na sa ɓangaren Dr. Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata, malami a jami’ar Maitama Sule dake nan Kano, kuma masanin tattalin arziƙi, wanda ya kasance a cikin shirin ya ce, ko kaɗan babu hikima cikin yin wannan ƙari.

Inda ya ce, mafita kawai shi ne gwamnati ta janye wannan ƙari ko kuma ta samar da hanyoyin rage raɗadi ga al’umma.

To amma ga Malam Usman Hassan Jakara wanda ya wakilci ɓangaren al’umma cewa ya yi “Wannan ƙari ya zo musu ne a lokacin da basu shirya ba, a don haka, akwai buƙatar gwamnati ta sake nazartar wannan mataki”.

Mafi yawa daga cikin waɗanda suka kira waya a cikin shirin, da kuma waɗanda suka aiko da saƙonnin ra’ayoyinsu kan ƙarin farashin ta shafin Facebook na Freedom Radio Nigeria, sun nuna rashin goyon bayan su ga yin ƙarin farashin.

A farkon watan Satumban da mu ke ciki ne, kamfanonin samar da wutar lantarki a ƙasar nan, suka fara amfani da sabon farashin wutar lantarki a faɗin ƙasar.

Kamfanonin sun ce, “Sun ɗauki wannan mataki ne bayan sauyin da hukumar sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta kasa wato NERC ta yi”.

Sabon tsarin dai ya karkasa masu amfani da wutar zuwa gida biyar inda zai kasance kowa zai samu wuta daidai gwargwadon kuɗinsa, wato dai iya kuɗinka iya shagalinka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!