Labarai
Rasuwar Aminu Dantata babban gibi ne ga yan Najeriya- ACF

Kungiyar tuntuba ta Dattawan Arewa ACF, ta bayyana rasuwar Alhaji Aminu Dantata, a matsayin babban rashi ga mutanen Arewa da ma Najeriya baki daya.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar wadda Sakatarenta Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya sanya wa hannu ta bayyana Aminu Dantata, a matsayin fitaccen Dan Arewa da ya gawurta wajen aikin alheri.
Sanarwar ta ce, Alhaji Aminu Dantata, ya na daga cikin dattawan da suka jagoranci kafa kungiyar ACF a shekara ta 2000, kuma suka tabbatar ta tsaya da kafarta.
Kungiyar ta kuma ce, marigayi Alhaji Aminu Dantata, kwararren dan kasuwa ne, dan siyasa kuma uba da ya shuka alheri da dubban jama’a ke amfana.
Haka kuma ta cikin sanarwar, ACF ta mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da ma al’ummar jihar Kano da Arewa da Najeriya, da fatan Allah ya jikansa.
You must be logged in to post a comment Login