Labarai
Rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Kano
Hatsaniyar dai tafa a ranar juma’ar da tagabata da misalin karfe biyu na rana a dai-dai lokacin manoman ke massalaci sai makiyayan da ake zargen gaiyatosu akai sama da mutum Ashirin tare da garken Shanuwansu suka durfafi gonakin manoman inda sukai masu barna da dama akan amfanin da suka noma
Yayin da manoman suka Ankara ne sukai kokarin su dakatar da makiyayan daga barnar da suke musu sai wadannan makiyaya suka fidda makamai suka fara Sara da duka tare da harbi da kibbu akan manoman wanda har takai ga daya daga cikin manoman ya rasa ransa
Wani mai suna Murtala daya daga cikin wadanda abun ya faro akan sa ya bayyana mana yadda Rigimar ta samu asali tare da cewa shima kansa sun harbe shi a da kibiya da kuma hannunsa.
Cin zarafin Fulani makiyaya babu abinda zai janyo sai kara rura wutar rikici- Hassan Kukah
Eti-Osa: rikicin kabilanci ya raunata tare da hallaka wasu da ba’a san adadinsu ba
Taraba:An sanya dokar takaita zirga-zirga a garen Jalingo sakamakon rikicin kabilanci
Yayin da wakilin mu ya ziyarci asibiti don gane wa idanun sa kan yadda Malam Ubale wanda wakilin mu Umar Lawal Tofa ya same shi a kan gadon asibiti cewa ya yi wanda aka kashe dan Uwan sane kuma ya kasance dan bijilanti sakamakon sun ganshi cikin kaki sai suka afaka masa.
Haka shima Mahaifin Usman da yarasa ransa a hannun makiyayan ya bayyana al’hininsa dan gane da yadda yaji rasuwar dan nasa, yana mai cewa abun bakin ciki ne matuka.
Ko da wakilin mu Abba Isa Muhammad ya tuntubi kakkakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da afkuwar al’amarin, yana mai cewa tuni rundunar ta dauki matakin da ya dace.
Masu fashin baki kan al’umar yau da kullum sun bayyana cewar kamata yayi gwamnati da jami’an tsaro da tashi tsaye domin dakatar da kai irin wannan hare-haren.