Labarai
Rikicin shugabanci : Ganduje ya gargadi daliban birnin Kano
Ma’aikatar sharia ta jihar Kano ta gargadi kungiyar daliban karamar hukumar birnin Kano da su guji shigar da al’amuran siyasa a cikin kungiyar.
Kwamishinan sharia na jihar Kano Barista Musa Abdullahi Lawan ne ya yi wannan gargadi ya yin wata ziyara da kungiyar suka kai ofishinsa.
Ya kuma shawarce su da su guji daukar doka a hannunsu domin hakan baya haifar da komai sai rudani.
“Kwamishinan sharia cewa yayi kasancewar anyi zabe daga bayane kuma akasami rabuwar kungiyar biyu lallai ya kamata su dauki matakin sharia karsu su dauki doka a hannun su”
A nasa bangaren shugaban dattawan kungiyar Khalifa Magaji Sa’idu, ya ce, sunje Ma’aikatar sharia ce domin kai korafin su bisa yadda aka raba kungiyar gida biyu.
“Shugaban kungiyar cewa yayi kasancewar duk kan su masu kaunar cigaban karamar hukumar ne sauran matasa suzo su yi tafiyar kungiyar domin ciyar da dalibai gaba”
Da yake jawabi shugaban kungiyar Kwamred Nafi’u Zaitawa, kira ya yi ga ‘yan kungiyar da su hadakan su rika tafiya tare domin ciyar da harkokin ilimi a karamar hukumar gaba.
“Sun kokane bisa yadda wasu a gefe guda suka raba musu kan kungiyar duk da irin wahalar da suka sha kafin ayi zaben domin sama da shekaru 11 ba’a gudanar da zaben kungiyar dalibai ba a kamaramar hukuma”
Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewa, a baya-bayan nan ne kungiyar daliban ta karamar hukumar birnin Kano suka dare gida biyu sakamakon rikicin shugabanci da ya kaure a tsakaninsu.
You must be logged in to post a comment Login