Labarai
Rudani ya kunno kai tsakanin Rundunar Sojin kasar
Rudani ya kunno kai tsakanin Rundunar Sojin kasar nan da ta ‘yan-sanda kan ko waye yake da alhaki bisa sace ‘yan matan Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Dapchi 110 a Jihar Yobe, da aka yi ranar 19 ga watan Fabarairun nan da mu ke ciki.
Rundunar Sojin ta-bakin mataimakin Daraktan yada labaran dakarun Operation Lafiya Dole Kanar Onyeama Nwachukwu, ta ce zargin da aka yi wa Sojojin ba gaskiya bane, kuma ai tuni su ka harkokin tsaron yankin hannun ‘yan sanda domin komawa wani wurin.
Sai dai Rundunar ‘yan sandan ta musanta hakan bayan da kwamishinanta a Jihar Yobe Sunmonu Abdulmalik ya sanar da cewa babu lokaci da Sojojin suka taba shaidawa ‘yan sanda cewa za su bar yankin a hannun yan sandan.
A baya dai an jiyo gwamnan Jihar ta Yobe Ibrahim Geidam ya dora alhakin sace ‘yan matan Dapchin ga janyewar da Sojojin suka yi daga yankin.
Kanar Nwachukwu ya ce Rundunar za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana wajen ganin an samu kyautatuwar tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa Maso gabashin kasar nan da rikici ya daidaita.
A jiya dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta wajen ganin an ceto dukkannin mutanen da ‘yan Boko Haram suka sace.