Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An daure ‘yan Najeriya da dama a gidajen yarin kasar China saboda karewar takardun zaman su a kasar

Published

on

Babban jakadan Najeriya a kasar China Mista Wale Oloko, ya ce ‘yan Najeriya da dama na daure a gidajen yari daban-daban a yankin Guangdong saboda samun su da laifin zama a kasar bayan takardun su na shiga kasar sun kare.

Mista Oloko ya bayyana hakan ne a jihar Lagos inda ya ce an kama wasu ‘yan Najeriya ne saboda aikata laifukan miyagun kwayoyi  wanda ta kai ga har  an tsare su a gidajen yarin baya ga wadanda aka kama da laiyukan da suka shafi rashin izinin zama a kasar.

A cewar babban jakadan a halin da ake ciki yawan ‘yan Najeriya dake zaune gidajen yarin kasar ta China sun kai dari shida 600, kuma babu tantama idan adadin su zai zarce hakan a gidan yarin Guangzhou, yayin da wasu da dama suka gwammace  da a dawo da su gida Najeriya.

A don haka Mista Oloko ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina kai ziyara wasu sassan kasar China saboda takardun su na izini shiga kasar ya kare kuma  su yi biyayya  ga dokokin hukumar shiga da ficen kasar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!