Labarai
Rundunar Ƴan sanda a Kano ta tsaurara tsaro gabanin bikin Easter

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta ƙara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan Easter.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Adamu Bakori, ya yi kira ga Kiristoci su gudanar da bukukuwan cikin lumana da haɗin kai, tare da gujewa duk wani abu da zai kawo hargitsi.
Rundunar ta bayyana cewa ta baza jami’anta a wuraren ibada da sauran muhimman wurare domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma, an umarci dukkan jami’ai su ƙara ƙaimi wajen sa ido da tabbatar da tsaro a duk lokacin bukin.
A ƙarshe, rundunar ta buƙaci jama’a su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga hukumomi.
You must be logged in to post a comment Login