Labarai
Rundunar Civil Defence shiyyar Jigawa ta bukaci mutane su rika yin taka-tsantsan

Rundunar tsaro ta Civil Defence shiyyar jihar Jigawa, ta bukaci al’ummar jihar da su kasance masu taka-tsantsan da kuma kula da duk wata mu’amala da za su yi yayin bukukuwan karamar Sallah.
A cewar rundunar, hakan babban mataki ne na kara inganta tsaro a fadin jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SC Badarudden Tijjani Muhamud, ne ya bukaci hakan a zantawarsa da wakilin Freedom Radio Kano Abba Isah Yakasai.
You must be logged in to post a comment Login